Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Episodes
900 episodes
Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji
Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuc...
•
19:37
Irin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwar Kafintoci Dake Kano
Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gob...
•
18:46
Darasin Da Za a Yi Koyi Dashi Cikin Takaddamar Dangote Da Farukh Ahmed
Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai.Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama ...
•
18:45
Yadda Takunkumin Amurka Zai Shafi Tattalin Arzikin ‘Yan Najeriya
Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Wannan takunkumi, wanda...
•
16:25
Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas
Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda...
•
14:58
Yadda Matsalar Tsaro Ke Hana Mu Tafiye-tafiyen Kirsimeti
A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukuk...
•
15:19
Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, d...
•
15:19
Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin...
•
17:01
Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe
Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kam...
•
22:20
Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa
Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a ce...
•
24:44
Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta
Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin m...
•
28:58
Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe
A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa....
•
24:22
Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.&...
•
24:25
Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi ...
•
21:42
Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake...
•
23:35
Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Sa...
•
24:18
Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu
Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Yayin da...
•
25:05
Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu.Irin wadanna...
•
19:29
Matsayar Doka Kan Taron Da Jam'iyyar PDP Ta Gudanar
Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu.Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta ...
•
25:28
Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani....
•
27:14
Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga g...
•
26:50
Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Kungiyar ASUU
A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙur...
•
25:07
Dalilan Yaduwar Cutuka A Irin Wannan Lokaci
Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci?<...
•
27:47