Najeriya a Yau

Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget

May 23, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
Show Notes

kawo yanzu dai kasuwar daliget ne ke ci a kasuwar siyasar  Najeriya, saboda karatowar zabukan fidda gwani a jamiyyun siyasar kasar.

To sai dai kuma hankali ya koma kan gyaran da sabuwar dokar zabe ta yi kan wane ne daliget a zaben fidda wakilan da zasu wakilci jam'iyyun siyasa a zaben badi.

Muna tafe da karin bayani kan dokar da ta tan-tan ce wane ne daliget da kuma fashin bakin cukumurdar da ta dabaibaye zabukan fidda gwanin da ake kokarin shiryawa.