Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget
•
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
kawo yanzu dai kasuwar daliget ne ke ci a kasuwar siyasar Najeriya, saboda karatowar zabukan fidda gwani a jamiyyun siyasar kasar.
To sai dai kuma hankali ya koma kan gyaran da sabuwar dokar zabe ta yi kan wane ne daliget a zaben fidda wakilan da zasu wakilci jam'iyyun siyasa a zaben badi.
Muna tafe da karin bayani kan dokar da ta tan-tan ce wane ne daliget da kuma fashin bakin cukumurdar da ta dabaibaye zabukan fidda gwanin da ake kokarin shiryawa.