Najeriya a Yau

Rayuwata Da Tsohon Ciki A Hannun Maharan Jirgin Kasa

May 27, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Rayuwata Da Tsohon Ciki A Hannun Maharan Jirgin Kasa
Show Notes

Harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga Maris ya rutsa da mata 18 ciki harda masu ciki. 

Wadansu matan sun haihu a cikin daji a hannun maharan, sannan sun sako wata mai cikin da ke sa ran haihuwa ko yau ko gobe.

Mai cikin da ta kubuta tayi mana bayanin yadda ta rayu a hannun maharan, ta kuma bayyana mana bukatar maharan.