Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Da Matasan Najeriya Ke Raina Jari
June 03, 2022
•
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
A halin da ake ciki na rashin aikin yi a gwamnatin tarayya da na jihohi, matasan Najeriya na cigaba da kukan abin yi sakamakon rashin jari domin fara sana'a.
Ko da yake wadansu na ganin ba jari matasan Najeriya ke bukata ba, lura da cewa jari domin fara sana'a baya kadan in anyi la'akari da bayanan da wadansu 'yan kasuwan ke yi.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da matasan ya kuma ji ta bakin 'yan kasuwa domin neman mafita.