Najeriya a Yau

Yadda Matasa Za Su Mori Tsare-Tsaren Bayar Da Bashi

June 06, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Yadda Matasa Za Su Mori Tsare-Tsaren Bayar Da Bashi
Show Notes

Matasa da dama na fama da rashin sanin hanyoyin samun bashi domin fara sana'a. 

A 'yan shekarun nan Gwamnatin Najeriya ta bayarda bashi ga manoma da masu kanana da manyan sana'a, sai dai da yawa matasan kasar na cewa basu san yadda ake neman wannan bashi ba, wasu kuma su ce in ma sun nema basa samu. 

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko hanyoyin da mai bukatar bashi domin fara sana'a zai bi domin samu a cikin sauki.