Najeriya a Yau

Kalubalen ’Yan Takarar Shugabancin Najeriya A 2023

June 09, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Kalubalen ’Yan Takarar Shugabancin Najeriya A 2023
Show Notes

A ranar Laraba 8 ga watan Yuni, 2022 Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kammala zaben fid-da gwanin da zai yi mata takara a babban zaben 2023.

Kasantuwar akwai jam'iyyun hamayya da ke hankoron hankade jam'iyyar APC din daga karagar mulkin kasar, ko wadanne kalubale ’yan takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya ke fuskanta?

Ku biyo mu domin sauraron irin fata da magoya bayan ’yan takara ke yi wa gwanayensu, tare da bayanan kalubalen da ke gaban ’yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben mai zuwa.