Najeriya a Yau

Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana

June 10, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana
Show Notes

A yayin da damina ke kara kankama a Najeriya, hankalin manoma ya koma gona da yadda za su samu takin zamani.

Sai dai kuma tsadar da takin ke yi a halin yanzu na neman tilasta wa da yawa daga cikinsu fasa noman.

Mun tattauna da wani kamfani mai sarrafa takin zamani domin jin dalilin da taki ya yi tashin gwaron zabo, mun kuma tuntubi wani malamin gona domin sanin ko akwai wata dabara da manoman za su yi domin yin noma a wannan hali da suke ciki.