Ranar 12 ga Yuni na 2022 mulkin dimokuradiyya ke cika shekara 23 da kafuwa a Najeriya ba tare da samun wani cikas ba.
A wadannan shekaru idan an saka kasar a fai-fai, cigaba aka yi ko kuma baya, mene ne ake bukatar a gyara a tafiyar da dimukuradiyya Najeriya.
'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan yadda su ke kallon yanayin mulkin a Najeriya, sannan mun tuntubi masana domin sanin abinda ya kamata a gyara a tafiyar mulkin kasar.