Najeriya a Yau

Inda Dalar Shinkafar Najeriya Ta Yi Aure Ta Tare

June 16, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Inda Dalar Shinkafar Najeriya Ta Yi Aure Ta Tare
Show Notes

Kusan wata biyar kenan da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da dalar shinkafa a babban filin tashin da saukar jiragen sama na Nmadi Azikwei a Abuja.

Taron bikin kaddamar da wannan dala dai ya janyo hankalin jama'ar kasar musamman yadda labaran adadin  buhun shinkafa miliyan daya da dubu dari biyu da aka gina wanna dala da su. 

Ance anyi wannan dalar ne da zimmar kawo karshen tashin gwauron zabbin da farashin shinkafar ke yi ne a kasar, amma har yanzu 'yan kasar sun ce  basu gani a kasa ba.

Ina dalar tayi aure ta tare?