
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Tasirin Rediyo Ya Sauya Al’ummar Duniya
•
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
Ranar 13 ga watan Fabrerun kowace shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar Rediyo ta duniya.
Gudummuwar da Rediyo ya kawo ta fi gaban a nanata ga mutanen karkara da na birni.
Albarkacin Ranar Rediyo, shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan wasu batutuwa a wannan rana.