
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hukuncin Dauri Kafin A Rataye Abdulmalik Bai Mana Ba —Dangin Hanifah
Iyayen karamar yarinyar nan Hanifa Abubakar, wadda malaminta ya sace sannan ya kashe ta a Kano, sun ce ba su gamsu da hukuncin daurin shekara biyar kafin a zartar mishi da hukuncin rataya ba.
A ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2022 kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko da abokinsa wurin kisan Hanifa hukuncin dauri a gidan gyaran hali da kuma kisa ta hanyar rataya bayan sun cinye wa’adin da aka diba musu.
Wannan hukunci, da aka yanke bayan wata shida ana shari’ar kisan na ci gaba da samun sharhi daga bakin jama’a, ciki har da dangin Hanifa, wadda Abdulmalik Tanko ya halaka.
Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da kuma dangin marigayiya Hanifa kan wannan hukunci. A yi sauraro lafiya.