
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Ba Zan Iya Daina Sa Hijabi Ba
•
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
Zamani ya zo da waɗansu ke yi wa mace mai saka hijabi kallon wacce bata cika ba, ko kuma wacce bata waye ba.
Shin ko har yanzu akwai matan da suka ji suka gani kan sanya hijabi?
Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci ya tattauna da waɗansu fitattun mata da suka yi fice a ilimin zamani amma kuma suna saka hijabi, mun tattauna kan dalilansu, mun kuma ji ta bakin malamai kan yadda hijabi yake a addinin Musulunci. Ku biyo mu sannu a hankali.