Najeriya a Yau

Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya?

Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi.

To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.