Najeriya a Yau

Guraben Aiki Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Duk da kukan rashin aikin yi da ako da yaushe ke cigaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, wadanda zasu cike guraben ayyukan ne suka yi karanci a Najeriya.


Alkaluma na cigaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun kasar a kowace shekara.
A yayin da da yawa basa samun aikin yi, so tari akwai dimbin guraben ayyuka da babu masu cike su don babu kwararrun da ake bukata.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai tattauna ne kan guraben ayyukan da aka kasa cike su da kuma nemo hanyoyi don magance matsalar.