Najeriya a Yau

Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Mallakan Muhalli na daya daga cikin burin kowanne dan Najeriya.
Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu.


Kananan ma’aikata da mafi karancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar dasu, ko tufatar dasu ba, ballantana har suyi tunanin mallakan muhalli nasu na kashin kansu.
Sai dai masana na bayyana cewa marasa karfin ma na iya mallakan nasu muhallin daidai ruwa daidai tsaki.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan hanyoyin da mai karamin karfi zai bi don mallakan muhalli a Najeriya.