
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
Sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arzikin alumma.
Alumma da dama musamman a wannan lokacin na kara bayyana alfanun koyan sana’ar hannu don dogaro da kai maimakon dogara da aikin gwamnati ko na kamfani.
Sai dai ana zargin wasu masu sana’ar hannu da rashin cika alkawari a wurin sana’ar su.
Irin wadannan masu sana’ar hannun teloli na daga cikin su, wadanda a mafi yawan lokuta ake zargin su da rashin cika alkawari musamman a lokutan bukukuwa na musamman.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan dalilan da suka sa telolin basa cika alkawari.