
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Illar Sare Itatuwa Ga Canjin Yanayi Da Lafiyar Mu
Shekaru da dama kenan da hukumomin duniya ke gudanar da tarurruka da dama kan zakulo hanyoyin da za a kawo karshen dumamar yanayi a duniya.
Dumama ko canjin yanayi na cigaba da barazana ga duniya, inda ake samun sauye sauye ga yanayi da wasu abubuwa da masana ke bayyana ka iya kara ta’azzara in ba’ayi wani abu a kai ba.
Daya daga cikin abubuwan da masana suka bayyana dake kawo wannan matsala itace yadda alumma ke kada itatuwan da aka dasa ba tare da lura da illar da hakan ke jawowa ga muhalli ba.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan illar sare itatuwa ba tare da dasa wasu ba kan sauyin yanayi da kuma lafiyar mu.