
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Kasuwanci Ke Kasancewa Gabani Da Cikin Ramadana
Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane sune kasuwa’.
Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikin su na daya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so.
Sai dai da Zarar ance watan Ramadana ya kama wasu daga cikin kasuwanci kan samu nakasu, inda wasu kuma ke samun habbaka.
Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma habbaka a wasu sa’anni.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda wasu kasuwanci ke habbaka da kuma yadda wasu ke samun koma baya cikin watan Azumin Ramadana.