Najeriya a Yau

Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Kasa Kiranye

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Mulkin demokradiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin dan adam.
A lokacin da ta baka damar tsayawa don a zabe ka kan wani mukami, kazalika ta baka damar zaben wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka.


Wani abun da demokradiyyar ta baiwa alumma dama a kai kuma shine na yin kiranye ga wakilan da suka zaba musamman idan wadannan wakilan basa biya musu bukatun da suka tura su a kai.
Tuni dai alummar kogi ta tsakiya suka fara kada kuri’un kiranye ga sanatar da suka aike ga majalisar dattawa bisa dalilai nasu na kashin kan su.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan matakai da sharuddan da ake cikawa don yin kiranye ga ‘yan majalisa.