
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Halin Da Matasa Suka Tsinci Kan Su A Najeriya
Yau a Najeriya da yawa daga cikin matasa na fuskantar kalubale musamman wajen biya ma kan su bukatun su na yau da kullum sakamakon yanayin tattalin arzikin kasa, rashin aikin yi da kuma tsadar rayuwa.
A wasu lokutan irin wadannan matasa sun yi karatu, wasu ma na da sana’oin su na hannu amma rashin aiki mai gwabi da zai biya musu bukatun su na cigaba da yin barazana da irin halin da suke tsintar kan su a ciki.
Wannan matsayi da matasan kasar nan suka tsinci kansu a ciki na cigaba da tura su cikin kuncin rayuwa.
Shirin Najeriya A Yau na wanna rana zai yi Nazari ne kan irin kalubalen rayuwa da matasan kasar nan ke tsintar kan su a ciki musamman a farko farkon rayuwar su.