
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Gabani Da Ranar Sallah
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
Lokutan sallah kamar yadda aka sani lokacin ne na farin ciki, nuna godiya ga ni’imar da Allah yayi mana da kuma bauta.
Kazalika lokacin ne da zamu lura da tabbatar da aiyukan da zamu aikata su zama ingattattu.
Ko wadanne irin abubuwa ne mutane ya kamata su aikata kafin da kuma ranar sallah?
Wadanne hanyoyi za a bi don tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin sallah?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan abubuwan da musulmi ya kamata suyi gabani da kuma ranar sallah.