
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana
Watan azumin ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka hada da kara kaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da alumma da kuma falala masu yawa da basu misaltuwa.
Wani sauyi da watan azumin watan ramadana ke zuwa dashi shine canjin yanayin ciman alumma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma bude baki.
Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun wadannan canji, ta wadanne hanyoyi ne alumma zasu koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan ramadana?
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutum ya kamata yabi don komawa cin abinci yadda ya kamata bayan azumtar watan Ramadana.