Najeriya a Yau

Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Alqurani mai girma a cikin suratul Baqarah Allah ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharudda azumtar watan Ramadana.


Kamar yadda malamai suka sha fadi, wannan wata na dauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji.
Kazalika hadisai sun ruwaito kan falalar azumtar kwanaki shidda na watan shawwal, watan dake biye da Ramadan.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar dake akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan shawwal.