Najeriya a Yau

Mene Ne Tasirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi?

Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an kirkire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da kabilanci.


Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba'in da biyar da fara wannan shiri, jama’a da dama na tambaya: 
ko har yanzu shirin na da tasirin da aka kirkire shi domin shi?
Ko har yanzu bautar ƙasa NYSC na ci gaba da samar da haɗin kai da ake buƙata a Najeriya?


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan ko har yanzu kwalliya na biyan kudin sabulu kan kafa shirin bautar kasa?