
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Tasirin Da Dangantakar Yan Uwa Yake Ga Rayuwar Alumma
Irin dangantakar dake kasancewa tsakanin abokai na da matukar tasiri ga farin cikin wadannan abokai, ta yadda a wasu lokutan ma baka iya banbancewa tsakanin ‘yan uwan su na jini da kuma abokai.
Irin wannan dangantaka ya kamata ne ace ana samun shi a wurin wadanda suke uwa daya uba daya ko kuma wadanda suke uba daya.
Sai dai a yayin da wasu ke samun kyakkyawan dangantaka tsakanin su da yan uwan su na jini, wasu kuwa basa ga maciji tsakanin su da nasu ‘yan uwan da suke uwa daya uba daya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan irin tasirin da 'yan uwantaka ke dashi ga rayuwar mutum.