Najeriya a Yau

Sabbin Dabarun Hana Matasa Aikata Laifuffuka

Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. 
Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su.


’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa.


Ko yaya wannan dabara take aiki?
Wannan ne abin da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.