
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Me Ya Sa Matsalar Tsaro “Ta Gagari Gwamnati” A Najeriya?
A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga ɗimbin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu matsalolin na ƙara Kunno Kai.
Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar kalubale iri-iri kama daga hare-haren da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, zuwa ga sabbin kashe-kashe a wasu garuruwan jihohin Filato da Binuwai sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta bulla a jihar Kwara.
To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan kara kazancewar matsalar tsaro da hanyoyin magance su a Najeriya.