Najeriya a Yau

Me Ya Sa Matsalar Tsaro “Ta Gagari Gwamnati” A Najeriya?

Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga ɗimbin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu matsalolin na ƙara Kunno Kai.


Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar kalubale iri-iri kama daga hare-haren da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, zuwa ga sabbin kashe-kashe a wasu garuruwan jihohin Filato da Binuwai sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta bulla  a jihar Kwara.
To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro?


Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan kara kazancewar matsalar tsaro da hanyoyin magance su a Najeriya.