
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
Ko kun san tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shuaban Kasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa?
Kundin na Tsarin Mulkin Kasa ne dai kundin dokoki mafi karfi a Najeriya wanda ya kunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shuggabanni da ma al’ummar kasa.
Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gudanar da dukkan al’amuran kasa, haka Kundin ya ayyana karfin ikon da kowane shugaba yake da shi, da iyakarsa da ma yadda zai iya mika wannan karfin iko ga wani don gudanar da ayyukansa.
Shin takamaimai wanne aiki Kundin ya bai wa Mataimakin Shugaban Kasa?
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.