
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
“Dalilan Da Suka Sa Muke Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyya Mai Mulki”
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya shekar da ’yan siyasa daga banarori daban-daban suke yi.
A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ta jawo diga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaben 2027.
Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan Najeriya suke kokawa da yadda ake gudanar da mulki a kasa da yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC.
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi nazari a kai da nufin gano alkiblar da siyasar Najeriya take shirin fuskanta.