
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Tasirin Dangantaka Tsakanin Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka
A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma.
A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci gaban kasa.
Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan amshin Shata.
Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin banaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.