
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su
•
Idris Daiyab Bature
Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).
Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su.
Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya.
Yayin da ake bikin Ranar Yara, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan halin da ya yara suke ciki a yau.