
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hanyoyin Kauce Wa Barnar Ambaliyar Ruwa
•
Idris Daiyab Bature
Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane tare da lalata dukiyoyi a fadin Najeriya.
Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa dake Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Ko wadanne hanyoyi za a bi don kauce wa barnar ambaliya a Najeriya?
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.