
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya
•
Idris Ɗaiyab Bature
’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa.
Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka saboda jami’in ya ki ya mika wayarsa.
Ko me mahukunta suke yi don hana aikata wannan laifi?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.