Najeriya a Yau

Matakan Dakile Kisan Matafiya A Hanyoyin Kasar Nan

Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na kara tsananta, musamman a yankunan Arewa. 


Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya tare da kashe wasu daga cikin su a hanyar Abuja zuwa Kano, a kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi dake jihar Edo a hanyar su ta komawa gida, sai na kwanan nan da ya faru a jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya dake kan hanyar su na zuwa daurin aure.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da nufin gano matakan dakile afkuwar haka a nan gaba.