
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Da za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya a yanzu, to da dole a samar da karin gwamna daya da sabuwar majalisar dokoki, da sababbin ma’aikatun gwamnati, da sauransu.
Samar da wadannan kuwa abu ne da yake bukatar makudan kudi – akalla Naira biliyan 30 duk shekara.
Ko da jihar za ta iya sama wa kanta kudin shiga kuma, za ta bukaci tallafi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta tsaya da kafafunta.
Shin a halin matsin tattalin arzkin da take fuskanta yanzu, Najeriya tana da kudin da za ta reni sababbin jihohi kuwa?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abin da kirkirar sababbin jihohi a Najeriya yake nufi ta fuskar tattalin arziki.