
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Mene Ne Tasirin Nadin Mataimaka Na Musamman A Rayuwar Jama’a?
•
Idris Daiyab Bature
Wadanda aka zaba su rike mukaman gwamnati kan nada wasu mukarrabai don su taya su sauke nauyin da aka dora musu.
Wasu na zargin nadin baya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga wadanda aka nada saboda rawar da suka taka yayin yakin neman zabe.
Ko irin wadannan nade-nade na da wani tasiri ga rayuwar alumma?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naden masu taimakawa shugabanni da irin tasirin da suke dashi.