
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki
•
Idris Daiyab Bature
Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.
Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya.