
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abin Koyi Daga Rayuwar Marigayi Muhammadu Buhari-- Makusantansa
•
Idris Daiyab Bature
Rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa 'yan Najeriya da dama kaduwa duk da cewa ya jima yana fama da rashin lafiya.
Sanar da rasuwar ke da wuya, 'yan kasa suka fara bayyana ra'ayoyi daban daban akan abin da suka gani game da rayuwar tsohon shugaban.
Amma makusantansa sun bayyana wasu halaye game da shi wadanda ba kowa ne ya sani ba.
Sune kuma shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.