
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Da Suka Sa 'Yan Najeriya Ba Sa Samun Adalci
•
Idris Daiyab Bature
Rashin samun adalci a Najeriya ba ya rasa nasaba da cin hanci da rashawa a bangaren shari’a, inda ake zargin wasu jami’ai suna karɓar kuɗi kafin su yanke hukunci, kamar yadda manazarta suka bayyana. Ko mece ce gaskiyar wannan lamari?
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.