
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI?
•
Idris Daiyab Bature
Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba.
Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba.
Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dacewar sanya doka gane da yadda mutane za su rinka amfani da fasahar AI.