
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Cutukan Da Rumar Daki Ke Haifarwa Ga Jikin Mutum
•
Idris Daiyab Bature
Malaman kiwon lafiya sun bayyana yadda ruma ke yada matsalolin rashin lafiya ga lafiyar jikin mutum.
Musamman a lokuta irin na ruwa, ruma kan dabaibaye gidajen mutane da dama na tsawon lokaci wanda ka iya jawo matsaloli daban daban ga lafiya da kuma gidajen mu.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin matsalolin da ruma ke haifarwa ga lafiyar jikin mu.