
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Tinubu Ya Yi Adalci Ga Ayyuka Da Mukamai Tsakanin Kudu Da Arewa—Bayo Onanuga
•
Idris Ɗaiyab Bature
Kungiyar tuntuba ta Arewa ta zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin daidaito wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan.
Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga maida martani ga Kungiyar ACF.
Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar Tuntuba Ta Arewa?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.