
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Me Dokar Kasa Ta Ce Kan Karin Wa’adin Aiki Da Shugaban Kasa Keyi?
•
Idris Ɗaiyab Bature
Bayan Karin wa’adin aiki da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi ga kwanturola janar na hukumar hana fasa kwauri ta kasa Bashir Adewale Adeniyi ne dai lamarin ke ta shan suka daga mutane daban-daban.
Yayin da wasu ke ganin abinda shugaban kasan yayi daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan yayi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.
Ko me dokar kasa tace game da wannan Karin wa’adi da shugaban kasan yayi?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.