
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shekara Nawa Shugabanni Ke Bukata Don Cika Alkawarin Da Suka Dauka?
•
Idris Daiyab Bature
Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika.
Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka?
wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.