Najeriya a Yau

Halin Kunci Da ‘Yan Fansho Ke Ciki A Wasu Sassan Najeriya

Idris Daiyab Bature

Send us a text

A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da suke samu duk wata. 

Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin da ‘yan fansho ke ciki a wasu jihohin Arewacin Najeriya.