
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni
•
Idris Daiyab Bature
Manoma da dillalan hatsi suna ci gaba da nuna damuwa a kan yadda farashin kayan abinci yake kara karyewa a kasuwanni.
Su kuwa wasu ‘yan Najeriya jin dadi suke yi saboda yadda farashin yake ta sauka.
Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin hatsin yake kara sauka a kasuwanni?
Wannan shi ne batun da shiriin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna a kai.