
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10
•
Idris Daiyab Bature
Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu.
Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan bada jimawa ba zai dara hakan.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin cigaba ko akasin haka da harshen Hausa da aladunta suka samu cikin shekara goma.