
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Matakan Da Ciwon Suga Ke Bi Kafin Yin Illa
•
Idris Daiyab Bature
Mutane da dama basa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance ta kafin tayi tsanani.
Sau da yawa ciwon sai ta kai wani matakin da zatayi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da ita.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin tayi tsanani da kuma hanyoyin magance ta.